Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ali Nuhu Ya Nemi Afuwar Mutanen Daya Taba Batawa Rai Dasu Gafar Ceshi - Ramadan


Fitaccen jarumin fina-finan Kanyywood, Ali Nuhu, ya bukaci mutane da su yi masa gafara idan ya yi musu laifi, alfarmar watan azumin Ramadana.


Jarumin, wanda ya wallafa sakon a shafinsa na Instagram, ya ce a iya saninsa bai yi wa wani laifi ba, amma duk da haka yana neman gafara saboda ajizancin dan adam.

A cewarsa, "Wannan shi ne satin karshe na wannan watan nan Ramadana. Hakika na san akwai jama'ar Musulmai da dama wadanda wannan shi ne Ramadan dinsu na karshe a nan duniya.

Allah shi ne masanin fili da boye, watakila ina cikinsu.

"Don haka nake kara neman afuwa a wajen dukkan wanda yake da wani hakkinsa a kaina, da kuma duk wanda muka taba samun sabani. Ni dai na yafe wa kowa, kuma ina neman afuwa a wajen kowa da kowa.

Allah Ubangijinmu mai afuwa ne, mai rangwame ne. Kuma yana son masu rangwame daga cikin bayinsa. Allah yasa mu dace," in ji Ali Nuhu.

Za a iya cewa Ali Nuhu, wanda ake yi wa kirari da Sarki, ya fi kowanne dan wasan Kannywood mabiya, kasancewarsa mutumin da ya dade yana jan zarensa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia