Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An Gano Wani Littafin Boko Haram Mai Cike Da Siddabaru


A Najeriya rundunar jami’an tsaro na farar hula NSCDC da ke jihar Borno, ta ce ta gano wani littafi ko kuma kundi da mayakan Boko Haram ke amfani da shi wajen sauya tunanin mabiyansu musamman masu zuwa kai harin kunar bakin wake.


Shugaban rundunar Abdullahi Ibrahim, ya ce an samu littafin ne a dakin saukar baki na Dikwa wanda mallakar gwamnati ne.

Sai dai Ibrahim ya ki yin karin bayani kan yadda suka gano littafin, amma a cewarsa, wannan littafi da shi mayakan na Boko Haram su ke yin amfani wajen sauya tunanin mabiyansu.

“A ciki ake nunawa mutum idan ka yi amfani da wannan (littafi) harsashi ba zai huda ka ba, kuma idan aka kawo maka hari za ka bace, sannan idan ka je saka bam, idan ka saka sai ka bace.” Inji Ibrahim.

Ya kuma kara da cewa sun mika littafin ga malamai wadanda suka yi bincike akai, suka kuma gano cewa irin wannan siddabarun al’umar Banduma da ke kasar Chadi ne ke amfani da shi.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia