Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Babu Kabilanci A Batun Korar Da Aka Yiwa Wasu Manyan Hafsoshin Soji A NigeriaRundunar ba ta bayyana sunayen wadanda ta sallama ba

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotanin da ke cewa ta kori wasu manyan jami'anta domin rage yawan sojoji 'yan Kudu da kuma karfafa 'yan Arewa.


Wasu kafafen yada labarai sun zargi rundunar ta kokarin dakile 'yan Kudancin kasar da bayar da fifiko ga yankin Arewa, inda Shugaba Muhamadu Buhari ya fito.


Sai dai wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce "an yi wa sojojin 38 ritayar dole ne kamar yadda tsarin dokar aikin soji ta tanadar, ba wai saboda kabilanci ko addini ba".


Sojojin sun hada da "manjo janar-janar guda tara, birgediya-janar 10, kanar-kanar bakwai, laftanar-kanar 11 da kuma manjo guda daya," a cewar mai magana da yawun rundunar Kanar Sani Usman.


A sanarwar da ta fitar tun farko, rundunar ta ce an sami jami'an ne da laifin shiga harkokin siyasa da kuma hannu a cin hanci da rashawa da ya shifi badakalar sayen makamai.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia