Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Bita Da Kulle Ake Mana: Inji Shugaban Majalisa Bukola Saraki


Majalisar dattawan Nigeria ta zargi bangaren zartarwa da yunkurin kawo cikas ga dimukradiyya ta fuskar bita da kulli ga shugabannin majalisar.


Majalisar ta kuma ja hankalin kasashen duniya ga abin da ta kira wani yunƙurin banganren zartarwa da zai jefa dimokradiyyar Nigeria cikin hatsari.

A ta bakin kakakinta, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, majalisar ta yi wannan korafi ne saboda rahotanni dake cewa gwamnati na shirin gurfanar da shugaban majalisar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekeweremadu a gaban kotu, bisa zargin yin zagon kasa tare da yin jabun dokokin majalisar, a lokacin zaben shugabanninta.

Sanarwar wadda majalisar dattawan Nigeria ta wallafa a shafukanta na Facebook da kuma Twitter ta ce, matakan gurfanar da shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki da mataimakinsa a gaban kotu wani shiri ne na gwamnatin tarayya na murkushe bangaren majalisar.


Sanarwar ta kuma ce, gwamnatin tarayya tana daukar matakan ne da nufin sauya shugabannin majalisar dattawan.

Majalisar dattawan ta kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen ministan shari'a, Abubakar Malami,da ya daina yi musu katsalanda.

Da ma dai shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki yana fuskantar wata shari'ar daban, kuma bisa ga dukkan alamu wannan batu zai bude wani sabon babi na sa-in-sa tsakanin majalisar dattawan da bangaren zartarwa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia