Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Buhari Ya Gargadi Fayose Akan Matarsa AishaShugaban Kasa Muhamnadu Buhari Yayi watsi da wani kage da gwanan jihar ikiti yake yiwa matarsa, Inda Yake Dangan Tata Da Wata Badakalar Cin Banci Da Rashawa a kazar Amurka.

Inda Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, Yace bai kamata a bar fayose ya dulmiyar da yan Nigeria da zantukansa na karya da shaci fadi ba.

Sannan Ya Kara Da Cewa 'Muna Gargadi da kakkausar murya ga mista fayose ya san cewa Aisha Buhari nada 'yancin kare mutumcinta.

Sannan ya kara da cewa ya kamata gwamnan ya shiga taitayinsa ya sani cewa b banbancin siyasa ba lasisi ba ne na cin zarafin jama'a.

A Dai Ranar Litanin ne gwamna fayose ya shaidawa kafofin yada labarai cewa Aisha Buhari nada hannu a badakalar cin banci data hada da wani dan Majalisar dokokin Amurka William Jefferson da aka yankema hukunci a 2009.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia