Home

Music

Video

Kanny

Tags:

CBN Sabon Tsarin Canjin Kudi A Nigeria
Godwin Emefiele shugaban babban bankin Najeriya ya ce matakin zai fara aiki ranar Litinin

Babban bankin Najeriya CBN, ya sanar da wasu sabbin ka'idoji na hada-hadar kudaden waje a kasar domin karewa da kuma farfado da darajar Naira

Ka'idojin sun hada da kafa sabuwar kasuwa ta musamman wadda za ta rage bukatar kudaden kasashen waje da matsin lambar da kudin kasar ke fuskanta.


Zai kuma bai wa 'yan kasuwa tabbaci domin su san cewar za su samu kudade na kasashen waje da zarar sun bukata.

Babban bankin zai zabi wasu manyan 'yan kasuwa da zai dinga hulda da su, inda bankin zai zuba dala biliyan 10 ga wannan kasuwa.


Wannan mataki dai zai fara aiki ne a ranar Litinin 20 ga watan Yunin 2016.


A sakamakon hakan CBN zai janye gefe ya zama mai sa ido kan yadda abubuwa ke tafiya domin tabbatar da cewa komai na tafiya daidai.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia