Cin Hanci Nigeria An Kori Wasu Manyan Jamian Soji


Rundunar ba ta bayyana sunayen wadanda ta sallama ba

Rundunar sojin Najeriya ta kori manyan jami'anta da dama saboda zarginsu da aikata cin hanci da kuma shiga harkokin siyasa a lokacin zaben shugaban kasa a bara.

Ba a bayyana sunan jami'an da aka sallama ba, sai dai sanarwar da rundunar ta fitar ta ce daga cikin su akwai wasu masu mukamin janar guda biyu.

Sanarwar ta kara da cewa tuni Hukumar da ke Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin kasa Ta'annati ta EFCC ta gurfanar da wasu daga cikin jami'an agaban kuliya.

A watan Fabrairun da ya gabata, rundunar sojin ta sanar da sunayen manyan jami'anta 12 da ake bincika game da satar kudaden gwamnati.

Jami'an sun hada da tsohon babban hafsan sojin kasar Air Chief Marshal Alex Badeh.

An zargi Mr Badeh ne da wasu manyan jami'an soji da karkatar da kudaden da aka ware da niyyar sayen jiragen yaki, zargin da ya musanta.

Wasu rahotanni sun ce an ware kudaden ne a wani bangare na yakin da kasar ke yi da kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

A baya sojojin kasar da dama sun sha korafin cewa ba su da isassun kayan aikin da za su tunkarar mayakan kungiyar.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia