Home

Music

Video

Kanny

Tags:

EFCC : Naci Gaba Da Tsare Tsobon Shugaban Kostom Abdullahi Dikko Inde A Asibiti
Sabanin rahotannin da ake yayatawa, hukumar EFCC ta bayyana cewa tana tsare da tsohon Shugaban Kwastan na Kasa, Abdullahi Dikko Inde a asibiti a maimakon ofishinta.

Hukumar ta EFCC ta nuna cewa tun a ranar Alhamis Dikko Inde ya mika kansa ga hukumar, ya zo ne a cikin yanayin rashin lafiya, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibiti.

Ana dai tuhumar tsohon shugaban Kwastan din ne da laifin almundahanar Naira Bilyan 42 kuma tun a watan Janairu EFCC ke nemansa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia