Jaruma Rahama Sadau ta faɗa hannun 'ɗan yankan kai-Gareku MasoyaFitacciyar 'yar wasan Kannywood, Rahama Sadau, ta faɗa hannun ɗan yankan kai, a wani fim mai suna Ba Tabbas.


Hotunan da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta sun ja hankalin masu sha'awar fina-finan Hausa.

Fim ɗin, wanda Ali Gumzak ke jagoranta, ya haɗa fitattun 'yan wasa irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Saratu Gidado, Maryam Booth da Tijjani Faraga.

Rahama Sadau ta fito ne a matsayin Habiba, Ali Nuhu kuma a matsayin Adam, yayin da Sadiq Sani Sadiq ya fito a matsayin Amadu.

'Yar wasan ta fito ne a matsayin mai son abin duniya, lamarin da ya sa ta ki auren Amadu, wanda tun asali shi ne ke shirin auren ta.

Habiba ta mika soyayyarta ga Adam sakamakon kudin da yake ba ta, duk da cewa ba ta san cewa ɗan ƙungiyar asiri da yankan kai ba ne.

Adam ya yi amfani da damarsa inda ya kai ta gidan yankan kai, bisa buƙatar ƙungiyarsu ta asiri.

Sai dai daga bisani ta kubuta, amma duk da haka al'umma ba ta ƙarbe ta ba.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia