Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Gwamnatin Buhari Ta Lashe Kaso 54 Na Jin Ra'ayoyin Yan Nijeriya


GWAMNATIN SHUGABA BUHARI TA LASHE KASO 54 A SAKAMAKON JIN RA'AYIN 'YAN NIJERIYA DA AKA GUDANAR

Daga Rabi'u Biyora

'International Republican Institute (IRI)' wacce take da ofis a kasar Amurka, ta gudanar da zaben jin ra'ayin 'yan Nijeriya akan mulkin Shugaba Buhari na shekara dayar da ya yi akan karagar mulki.

Sakamakon jin ra'ayin ya nuna cewa kaso hamsin da hudu (54%) na mutanen da suka yi zaben sun aminta da gwamnatin Shugaba Buhari tare da kyakkyawan zaton alheri da suke yi wa mulkin.

Kaso talatin da bakwai (37%) na 'yan Nijeriya ba su aminta da salon mulkin gwamnatin Buhari ba, kuma mafi yawan wadanda basu aminta ba sun fito ne daga yankin Kudu maso Gabas wato yankin Inyamurai.

Babban Daraktan hukumar Mista John Tomaszewski shine ya bayyana wa 'yan jaridu sakamakon a birnin tarayya Abuja sannan ya kara da cewa mafi yawan 'yan Nijeriya sun aminta da gwamnatin Shugaba Buhari musammam idan suka yi la'akari da gwamnatocin baya da suka gabata.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia