Hukumar Yan Sandan Nigeria Ta Kama Wani Likitan Bogi A Abuja
Asibitin Luna da ke Gwarinoa a Abuja


'Yan sanda a Nigeria sun kama wani likitan bogi a Abuja babban birnin kasar, wanda ake zargi da tafiyar da wani asibiti na tsawon shekara 10 ba bisa ka'ida ba.


Ana zargin mutumin mai suna Moffat Akpan, da bude asibitin ta hanyar yin amfani da takardun bogi.


Mista Akpan dai yana aiwatar da ayyuka da suka danganci tiyata da karbar haihuwa da sauransu a asibitin.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara gano Mista Akpan ne tun a shekarar 2013 inda ya yi wa wata mata tiyata ta haifi 'yan biyu da suka zo a hade, wadanda daga bisani ya tura su babban asibitin kasa na Abuja National Hospital, inda suka mutu a can.


Ta kuma ce wani babban jami'i na kungiyar Likitoci ta Najeriya, Dakta Henry Okwuokenye, ya ce kungiyar ba ta bai wa Mista Akpan lasisin yin aikin likita ba, saboda gwamnati ba ta bai wa jami'ar da ya kammala damar bayar da horo ga dalibanta na wannan fanni ba.


Jaridar ta kuma ambato Mista Akpan yana cewa, ''A shekarar 2002 ya bai wa wani jami'in kungiyar likitocin naira dubu 15 domin ya samu takardar shaidar zama cikakken likita.''


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia