Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Hukumar Yan Sandan Nigeria Ta Kama Wasu Matasa

Hukumar Yan Sandan Jihar Nasarawa Ta Kama Wasu Matasa Bisa Zargin Su Da Amfani Da Takardun Makaranta Na Jabu A Yayin Neman Aikin Dan SandaInda Kuma Suka Kama Daya Bisa Zargin Satar Wayar Salula

Sudai Wadannan Matasa Ankamasu Ne A Lokacin Da Ake Daukar Masu Son Saiga Aikin Dan Sanda A Garin Lafiya Da Jihar Adamawa.

Kwaminshinan Yan Sandan Jihar Alhassan Mamoda, Wanda Ya Bayyana Wa Kamfanin Dillan Cin Labarai Na Nijeriya,Wannan Labari Ya ce Mutane Hudu Ne Aka Kama Bisa Zargin Su Da Amfani Da Takardun Makaranta Na Jabu, Inda Daya Cikon Na Biyar Din Ake Zargin Sa Da Satar Wayar Salula.

Inda Ya Bayyana Hakan Da Cewa Abin Mamaki Ne Kwarai Da Gaske A Sami Mai Neman Aikin Dan Sanda Da Laifin Satar Wayar Salula Tun A Inda Ake Tantancesu, Alhalin Shine Akesaran Zaiyi Aiki Tukuru Wurin Kare Dukiyoyin Alumma Da Lafiyarsu.

Sannan Kuma Ya Gargadi Masu Aikata Miyagun Laifuka Da Muguwar Dabi'a Dasu Shiga Taitayinsu.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia