Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kungiyar Tsagerun Naija Delta Avengers Sun Amince Su Tsagaita Wuta


Kungiyar Niger Delta Avengers (NDA), da ke fasa bututan man fetur na Najeriya ta amince ta tsagaita wuta har tsawon wata guda.


Kamfanin dillancin labara na Reuters ya ambato wata majiya a ma'aikatar man fetur din kasar tana tabbatar masa da labarin.

Yana da matukar wahala shawo kan NDA su shiga tattaunawar amma mun san samu mun yi hakan ta hanyar amfani da wasu hanyoyi domin cimma wannan zaman lafiya," a cewar wani jami'i wanda ba su bayyana sunansa ba.

Wasu daga cikin jaridun Najeriya ma sun rawaito wannan labari.

Sai dai kawo yanzu 'yan kungiyar ba su fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa sun tsagaita wuta ba.

Kungiyar ta Niger Delta Avengers dai ta dauki alhakin fasa bututan man fetur da dama, ciki har da na kamfanin Shell da Chevron.

Sau da dama kungiyar tana shan alwashin durkusar da harkokin man fetur na kasar.

Kwanakin baya 'yan kungiyar suka ce za su yi sulhu da gwamnatin kasar, inda suka nada wasu manyan mutanen yankin na Naijda Delta domin shiga tsakaninsu da gwamnatin.

NDA ta ce tana fafutika ne domin ganin an samu 'yanci a yankin na Naija Delta, wanda ta ce mazauna yankin ba sa cin moriyar arzikin man da Allah ya yi musu.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia