Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kwamitin Zakka Da Wakafi Na Jihar Sokoto Ya Tallafawa Marasa Galihu


Kwamitin Zakka Da Wakafi Na Jihar Sokoto Ya Tallafawa Marasa Galihu


Kwamitin zakka da wakafi na jihar Sokoto, ya tallafawa wasu mata da gajiyayyu da kayan sana'oi da tallafin kudade.

A cikin jawabin ta, babbar bakuwa a wurin taron kuma matar gwamnan jihar Sokoto, Hajiya Maryam Mairo Aminu Waziri Tambuwal, wadda Hajiya Laraba Gambo Abdullahi ta wakilta, ta godewa Kwamitin tare da yin kira ga wadanda suka amfana da su yi aiki da tallafin domin samun ci gaba.

Kayayyakin da aka raba sun hada da kekunan dinki, injin nika da kuma katifu. Haka zalika an tallafawa wasu wadanda bala'in gobara ya fadawa da kudade da kuma wasu kayan amfani na gida domin su rage radadin hasarar da suka yi.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia