Masarauta Ta Yiwa Halima Atete Nadin Sarautar Gimbiyar Kanyywood


Anyiwa Halima Atete Nadin Sarautar Gimbiyar KannywoodRanar Asabar da ta gabata aka yi bikin nadin sarautar gargajiya ga wasu mashahuran masu shirya finafinai, inda aka nada Shugaban Kungiyar Arewa Filmmakers Association (AFMAN), reshen Jihar Kano, Jamilu Yakasai, wanda aka fi sani da ‘Dakan Daka’ a matsayin Saradaunan masana’antar shirya finafinai.

A yayin da aka nada fitacciyar jarumar Halima Atete a matsayin Sarauniyar masana’antar shirya finafinan Hausa. Taron dai ya gudana ne karkashin AFMAN, reshen jihar Zamfara.

Da yake gabatar da jawabinsa shugaban kungiyar reshen jihar Zamfara Alhaji Sani Garba Gusau ya bayyana dalilansu na yin wannan nadi, inda yace sun yi la’akari da irin gudunmawar da wadannan zakakurai ke bayarwa ga ci gaban wannan masana’anta, haka kuma ya tabbatar da cewar gogewa da kuma sadaukar da kai na wadanan mutane ne sandiyyar yi masu wannan sarauta. Shugaban ya ce, “Mun zabo mutanen daga jihar Kano, Katsina, Kebbi da Borno domin ba su wadannan sarautu, a karshe ya tabbatarwa da wadanda aka nada a wadanann sarautu daban daban cewar da zarar mai matarba sarki ya dawo daga Ummara, za a gabatar da wadannan mutane domin sa albarkarsa.”

Da yake zantawa da Jaridar Leadership Hausa jim Kadan da kammala nadin nasu, Sardaunan Kannywood ya bayyanawa cewa ko shakka babu wannan abin farin ciki ne wanda kuma shi ne irinsa na farko.

Dakan Daka ya ci gaba da cewar shugabannin kungiyar tasu reshen jihar Zamfara ne suka zauna da sarakunan sun a jihar Zamfara, inda suka bukaci amincewarsu domin nada mana wannan sarautu. Daka aka tambaye shi yadda taron ya gudana, shugaban na AFMAN ya ce an gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da kuma nasara.

Ita ma a nata bangaren Sarauniyar ta Kannywood Hajiya Halima Atete ta bayyanawa wakilinmu farin cikinta bisa samun wannan sarauta. Ta ce ko shakka babu samun wannan sarauta ya tabbatar mata da kwazon da suke nunawa a cikin masana’antar shirya finafinan. Daga nan ta kara da cewa, “Na yi matukar farin ciki, kuma na sanya hakan a cikin manyan abubuwan tarihin da ba zan taba mantawa da shi a rayuwata ba.”


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia