Mayakan Boko Haram '700 Sun Mika Wuya - Nigeria


Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram 700 ne suka mika wuya ga gwamnati kawo yanzu.


Mayakan kungiyar, wacce ke kokarin kafa daular Musulunci a kasar, sun ajiye makamansu ne a cikin wata shida da suka gabata, a cewar mai magana da yawun rundunar tsaro ta kasar.


Birgediya Janar Rabe Abubakar ya shaida wa BBC cewa mayakan sun fito ne daga sassan kasar da dama da ke fama da matsalar ta Boko Haram.A baya dai gwamnatin Najeriya ta fito da wani shiri inda a karkashinsa za a rinka sauya wa 'ya'yan kungiyar tunani domin sake komawa su ci gaba da gudanar da rayuwarsu a cikin jama'a.


Fiye da mutum 20,000 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da kungiyar ta kaddamar yaki da gwamnatin Najeriya a shekara ta 2009.


A yanzu Boko Haram, wacce ta mika wuya ga kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS, ta rasa kusan dukkan yankunan da take iko da su a baya sakamakon matsi daga sojojin hadin gwiwa na kasashen yankin Chadi.


Sai dai har yanzu ta kan kai hare-hare musamman na kunar bakin wake a wasu sassan yankin.


Ko a yammacin ranar Alhamis, wasu mayaka da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Diffa na Jamhuriyar Nijar, sai dai babu wasu cikakkun bayanai kan irin barnar da harin ya haifar.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia