Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Hotuna Muhammadu Buhari Ya Dawo Daga Birnin Landon


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinyar da ya je yi a birnin London a ranar Lahadi.


Shugaban ya sauka ne a babban filin jirgin sama na birnin tarayya Abuja, da misalin karfe biyar na yamma.


Manyan jami'an gwamnati da dama ne suka tarbi shugaban a lokacin da ya sauka.


Ana kuma sa ran zai koma bakin aiki a ranar Litinin, domin cigaba da tafiyar da al'amuran kasar.


A makon da ya gabata ne shugaban, mai shekara 73, ya tafi London domin yin jinyar ciwon kunnen da yake fama da shi bisa shawarar likitocinsa na Najeriya.


Tun da fari an shirya shugaba Buhari zai dawo ranar Alhamis da ta gabata ne, amma sai ya jinkirta dawowar tasa zuwa ranar Lahadi domin ya kara hutawa.


A ranar Alhamis din ne kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya sanar da cewa Buhari yana nan lafiya kuma zai dawo ranar Lahadi.


KAllA CIKIN HOTUNA..


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia