Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Sojojin Nigeria Sun Kashe Yan Boko Haram '7 Sun Kama' 11 A RayeA yayin wata farauta da dakarun sojojin Nijeriya suka fita a tsakanin kauyen Bitta zuwa Gambori dake jihar Borno a jiya Lahadi, sojojin sun yi nasarar fatattakar 'yan Boko Haram a kauyen Bulajani.

Saidai a yayin da sojojin suke kan fatattakar 'yan bindigan sun ci karo da wani abin fashewa, wanda hakan ya sa biyar daga cikin sojojin suka samu rauni. Amma duk da hakan sojojin sun kashe biyar daga cikin 'yan bindigan,

yayin da kuma da yawa daga cikin su suka tsira da raunin harbin bindiga.

Haka kuma sojojin sun gano wani abun fashewa da 'yan bindigan suka dasa a kauyen Madube.

Sojojin da suka samu raunin an garzaya da su asibitin dakarun 23 Burgediya dake garin Yola domin duba lafiyarsu.

A wani labari makamncin haka, dakarun 22 Brigade Garrison sun fita wata farauta a kauyen Albanya dake kusa da garin Dikwa-Marte. Inda sojojin suka fara da 'yan bindigan a daidai kauyen Sinabaya dake kan titin Marte-Kaje a karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

A yayin artabun an kashe uku daga cikin 'yan Boko Haram din tare da kama sha daya daga cikinsu.

Haka kuma sojojin sun kwato makamai da dama na 'yan bindigan tare da babura da waya.

'Yan Boko Haram din da aka kama a raye an garzaya da su hedikwatar sojojin domin ci gaba da bincikensu.


KALLA CIKIN HOTUNA...


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia