Tsohuwar Ministan Nigeria Diezani Ta Maida Martani Ni ba ɓarauniya ba ceAna zargin Diezani da tafka almundahana lokacin da take ministar man Najeriya

Tsohuwar ministar mai ta Nigeria, Diezani Alison-Madueke ta musanta zargin da gidan Talabijin na Al jazeera ya yi mata cewa ta tafka cin hanci lokacin da take rike da mukamin.

A rahoton, Aljazeera ta yi zargin cewa Diezani Alison Madueka na da gida a Abuja da ya kai dala miliyan 18 da gwala-gwalai da darajarsu ta kai dala miliyan biyu.

Hukumar da ke Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin kasa Ta'annati, EFCC, ta kwace kadarorin tana zargin an mallake su ne da kudaden cin hanci.

Misis Alison-Madueke ta ce dama ta na da arzikinta tun kafin ta zama minista kuma za ta iya mallakar kayayyakin more rayuwa inda ta bayyana masu zarginta da cin hanci a matsayin marasa imani.

Diezani ta ce "ba wannan ne karo na farko da aka yi yunkurin bata min suna a idon al'umma ba".

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Misis Madueke ta ce rahoton wanda aka hada ba tare da wani shaida ba, an yi ne da zummar bayyana ta a matsayin mai aikata mugayen laifuka.

Ta kara da cewa "yaushe ya zamo lafi don mace mai kima irin ta wa ta mallaki gwala-gwalai".


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia