Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Wata Mata Ta Burma Ma Mijinta Wuka A Ciki Sabo Da Yayi Mata KishiyaDaga Ma'awuya Abubakar Zurmee

Ana zargin wata mata mai suna Amina Banaga Maru dake garin Gusau babban birnin jihar Zamfara da niyar hallaka mijinta ta hanyar soka masa wuka a ciki har sau uku.

Lamarin wanda ya auku a jiya Litinin, bincike ya nuna cewa matar ta yi niyar halaka mijin nata ne saboda tsantsar kishi.

Bayanan da muka samu sun tabbatar mana da cewa ana zargin Amina ta yi wa mijin nata wannan danyen aikin ne saboda niyyar da yake da ita na yi mata kishiya.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka mijin nata yana asibiti ana yi masa aiki, inda yake cikin halin rai-kwakwai-mutu -kwa-kwai.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia