Yadda Tauraruwar Manyan Directors Biyu Take Kadawa A Social Media Aminu Saira

AMINU SAIRA DIRECTOR DIRECTOCIAminu Saira ya shahara wajen yin manyan fina-finai


Malam Aminu Saira, kamar yadda aka fi sanin sa, fitaccen mai hada fina-finan Kannywood ne, kuma ya taba shaida wa BBC cewa babu abin da yake burge shi kamar hada fim din da zai ilimantar da mutane.

Aminu Saira ya hada fina-finai da dama cikin su har da 'Daga Ni Sai Ke', wanda yar burge dimbin masu kallo. Yana da mabiya 94,000 a Instagram.

FALAHU A DORAYI BABA UBAN TALAKAWA DATTIJON DATTIJAN KANNYWOODAna yi wa Falalu Dorayi lakabi da "Dattijon Industry"


Ana yi masa lakabi da "Dattijon Industry" saboda halayensa na dattaku da tsayawa kan gaskiya. Falalu Dorayi ya yi fice wajen bayar da umarni, sannan yana fitowa a matsayin jarumi.

Ya taba shaida wa BBC cewa babban abin alfaharinsa shi ne "yadda wani ya Musulunta ta hanyar fim din da na hada".

Masu bibiyar masana'antar Kannywood sun ce Falalu Dorayi ba ya wasa da aiki da kuma biyan mutum idan ya kammala aikinsa. Yana da mabiya sama da 62,000 a shafin Instagram.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia