Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Yanzu Haka Shekaru Goma Sha Bakwai Kenan Da Rasuwar Alhaji Mamman Shata


Shekaru 17 Da Rasuwar Marigayi Dakta Mamman Shata Katsina


A ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 1999 ne, Allah ya yi wa shahararren mawakin Hausan nan, Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina rasuwa a wani asibiti mai zaman kansa dake birnin Kano.

A jiya Asabar, 18 ga watan Yuni shekara ta 2016 marigayi Shata yake cika shekaru 17 cif-cif da rasuwa, muna addu'ar Allah ya gafarta masa, amin.

Ana cigaba da tunawa da basirar marigayi Shata wanda ya samu lambar girmamawa ta Dakta a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, da wakarsa ta marigayi Ciroman Gombe, wadda ta zama karin magana a tsakanin Hausawa, inda yake cewa "Kowa ya mutu bai yi sauri ba, mu da muke nan ba mu dade ba, sai munzo Ciroman Gombe".


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia