Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Yaron da Kishiyar Mahaifiyar Sa Ta kakkaryawa Kafafu Ya Samu Tallafi-Aisha Buhari


Daga Hamisu Nasidi Baban Auwaab


A watan da ya gabata ne labari mai firgita zuciya, mai tayar da hankali ya bayyana daga karamar hukumar Rimin Gadon jihar Kano cewa wata kishiyar uwa ta yi wa dan kishiyarta da yake ruko kisan mummuke.


Matar nan gaba daya ba ta so Yaron ya ci gaba da rayuwa ba, kuma burin ta koda zai rayu ta yi masa nakasar da ba zai iya wani amfani ba balle ya amfanar da waninsa. Shine dalilin da ya sa ta kakkarya hannayen sa da kafafunsa, ta kuma yanke harshensa tare da tsaga masa maraina.


Lallai wannan matar ba karamar "yar daba ba ce kuma gogaggiyar mara tausayi ce, cikakkiyar mara imani, wadda kafin ita bana jin an taba samun mai irin taurin zuciyar ta da rashin imaninta. Kawai dan iskanci ki kama yaron da ko mahaliccin sa bai dora masa wani hukunci ba ki cake masa ido. Kai... Kai... Kaiii me kike tsammani da rayuwa ne?


Rashin mutuncin su ne ya fitar da babar Musa daga dakinta, kuma suka kasa hakuri bayan bakin cikin da suka cunkusa mata na sakin ta, suka kara bakanta mata ta hanyar kwace mata dan karamin yaronta da bai wuce shekara biyu ba. Karshe suka so ta hadiyi zuciya ta mutu sabida sun nakasa mata yaro bayan sun kwace mata shi.


Burin su kada yaron ya taso ya amfanar da mahaifiyarsa, kada ta rayu da shi ya jikanta, sai Allah Ta'ala ya nuna musu cewa rayuwa a hannun sa take, kuma kowane dan Adam ba zai bar duniya ba sai ya cinye arzikinsa. Alamu sun nuna cewa Malam Musa yaro ne mai albarka a rayuwa kuma mai arziki. mutum ne za'ayi mai albarka insha Allah.


Ga albarkar sa nan ta fara bayyana, arzikin sa ya fara nasar mahaifiyarsa, ku kalli yadda manyan mutane da shugabannin al'umma suke tururuwar taimakonsa. Mahaifiyar ba ta taba mafarkin za ta ga Sarkin Kano ko gwamnan Kano ba. Amman cikin ikon Allah yau ga shi ta hau jirgin alfarma kwana a fadar shugaban kasa ta dalilin yaronta mai albarka.


Ta mallaki gida da kudade, ta kuma yi tozali da masu kaunar ta na gaskiya ita da yaronta. Ita kuwa waccen annamimiyar kishiyar tata tana can cikin gidan kaso ko gidan jarun a kulle.


Don haka a duk lokacin da mutum zai gina ramin mugunta inji Bahaushe........!!!


Allah ka karawa Musa Murtala lafiya da kwarin jiki ka kuma daukaka shi.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia