Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An bayar da belin Yunusa YellowWata babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya ta bayar da belin Yunusa Dahiru (Yunusa Yellow) bayan ya shafe wata shida a tsare.


Ana zargin sa ne dai da sace wata yarinya 'yar asalin jihar ta Beyelsa, Ese Oruru, sannan ya aure ta ba tare da amincewarta ba, kodayake ya sha musanta zargin.

Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara.

Kotun dai ta bayar da belin Yunusa ne bayan ya cika sharudan belin da aka gindaya masa.

Daya daga cikin lauyoyin da suka kare shi, Barista Huwaila ta shaida wa wasu kafafen watsa labarai na kasar cewa fiye da lauyoyi 100 ne suka yi fafutikar fitar da Yunusa, wadanda babban lauyan kasar Alhaji Yunusa Usman ya jagoranta.

 CIKIN HOTO BARRISTER Hawaila ALI
CIKIN HOTUNA YUNUSA DA MAHAIFIYAR SA..


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia