An bukaci Buhari ya kori Buratai daga mukaminsa - Nigeria


Duk da cewa Sojojin da buratai yake jagoranta suna ci gaba da yin nasara akan mayakan boko haram a Nigeria

Wani babban lauyan Najeriya, Mista Femi Falana, ya bukaci shugaban rundunar sojin kasar Laftanar Janar Yusuf Buratai ya sauka daga mukaminsa saboda mallakar gidajen da ya yi a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Mista Falana ya shaida wa BBC cewa bai kamata Janar Buratai ya ci gaba da zama a rundunar sojin kasar ba ganin cewa abin da ya yi ya saba wa dokar kasar.

Ya ce, "Dole Shugaba Muhammadu Buhari ya sa Buratai ya sauka daga mukaminsa ko kuma ya kore shi daga aiki sakamakon mallakar gidaje biyu da ya yi a kan tsabar kudi $1.5m sabanin dokar Najeriya."

"Ba zai yiwu ya mallaki wadannan gidaje da irin albashin da ake ba shi a domin kuwa darajarsu ta fi karfin albashinsa," in ji Mista Falana.

Babban lauyan na Najeriya ya ce ya kamata Shugaba Buhari ya sani cewa ba zai iya yaki da cin hanci da rashawa idan har bai nuna halin ba sani ba sabo ba, yana mai cewa "tunda shugaban kasar yana yaki da ta'addanci, dole ne ya hada da cin hanci da rashawa domin ya yi nasara."

Ita dai rundunar sojin kasa ta Najeriya, a wata sanarwa da kakakinta Sani Usman Kukasheka ya fitar, ta amince cewa Janar Buratai ya mallaki gidajen ne ta hanyar kudin da ya tara.

Ta kara da cewa wasu mutane da ke son tayar da zaune-tsaye ne ke son shafawa Janar Buratai kashin-kaji ganin irin nasarar da yake samu a yakin da yake yi da kungiyar Boko Haram.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia