Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An fara tono kudaden da wasu Barayin Gwamnati suka burne a turbaya-NigeriaAn Fara Tono Kudaden Sata Da Aka Turbude Cikin Gonaki A Abuja- Dogara

Shugaban Majalisar Waklilai, Yakubu Dogara ya tabbatar da cewa jami'an tsaro sun fara samun nasara a binciken da suke yi na gano kudaden sata da aka turbude a cikin kasa a wasu gonaki da ke Abuja.

Dogara ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da 'yan jaridu inda ya nuna cewa a halin yanzu an tono Naira Bilyan 1.5 a gonar wani babban mutum da ke Abuja inda ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ke satar kudaden da ba su bukatar su a rayuwa.

Ya kuma musanta zargin da ake yi na cewa yaki da rashawa da gwamnati ta kaddamar, an tsara shi ne da nufin muzgunawa bangaren adawa inda ya nuna cewa akwai na hannun damar shugaban kasa da a halin yanzu ake tuhumarsu kan rashawa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia