Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An Gano Sojojin Da Suka Bace A Filin Daga A Jihar Borno


An Gano Sojojin Da Suka Bace A Filin Daga A Jihar Borno


Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano wasu daga cikin sojojinta da suka bata samakon wata mummunar arangama da suka yi da mayakan Boko Haram.

An sake "gano biyar daga cikin sojojin" da suka bace a kwantan-baunar da aka yi musu a ranar Laraba, a cewar kakakin rundunar Kanar Sani Usman.

Ya kara da cewa cikin wadanda aka gano har da kwamandan da ke jagorancin tawagar wacce ta fafata da mayakan kungiyar a kauyen Guro Gongon da ke jihar Borno.

Tun a lokacin da lamarin ya faru, rundunar ta ce ta kaddamar da gagarumin farmaki domin gano inda suke.

Sai dai babu tabbas kan adadin sojojin da har yanzu ba a gano ba.

Kimanin sojoji 19 da 'yan kato-da-gora uku ne suka jikkata a lokacin gumurzun.

A 'yan kwanakin nan mayakan Boko Haram na kai hare-hare kan dakarun Najeriyar, duk da irin nasarar da dakarun ke cewa suna samu wurin murkushe su.

Fiye da mutane 20,000 ne aka kashe a rikicin wanda aka shafe shekaru bakwai ana fama da shi, yayin da sama da miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia