Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An Kirkiro Shafin Cin Zarafin Malamai Domin Shafawa 'Yan Film Kashin Kaji


An Kirkiro Shafin Cin Zarafin Malamai Domin Shafawa 'Yan Fim Kashin Kaji


Wannan Sanar Wan Ta Fitone Kai Tsaye Daga Daya Daga Cikin Shahararrun Yan Wasan Hausa Na Kannywood Wato Rabiu Rikadawa.

Bayan Samun Bullan Wani Shafin Facebook Mai Suna Northern Film Production Inda Shafin Ya Ya Shahara Wurin Cin Mutumcin Manyan Malaman Kasar Nan Musamman Malaman Kungiyar Izala. Ta Yadda Shafin Ke Yada Hotuna Marasa Kyan Gani Tareda Fadin Muna Nan Kalamai Akansu.

Haka Kuwa Ya Biyo Bayan Irin Gudun Muwar Da Wasu Daga Cikin Malaman Suka Bayar Wurin Kiraye Kiraye Da Khudubobi Da Sukayita Yi Domin Ganin An Soke Batun Ginin Katafaren Dandalin shirya fina-finai Da Gwamnatin Tarayya Zata Gina A Jihar Kano, Wanda Ake Yi Masa Lakabi Da FILM VILLAGE.

Gadai Abunda Rabiu Rikadawa Ya Wallafa A Shafinsa Na Facebook.

Salam, ni Rabiu Rikadawa mataimakin sakataren kungiyar jarumai ta Kannywood ina sanar da jama'a cewa, mu a masana'antarmu ta Kannywood, ba ma tare da wasu da suka bude wani shafi a Facebook mai suna "Northern Film Production"

Wandanan mutane suna aibata Malamanmu na sunna a shafin nasu. Suna rubuce-rubuce gami da saka wasu hotuna na batanci na malaman sunna.

Wannan abin da suka yi bai yi daidai ba, kuma ba da yawunmu suke yi ba, Hasalima bamu san ko su waye ba.

Soke 'films village' bai ragi masana'antarmu ba ko kadan, bare har mu yi fushi ko mu hasala da wani, balle ta kai mu ga yin batanci a gare shi.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia