An Soke Batun Gina Dandalin Shirya Fina-Finai Film Village A Kano

Muhammad Buhari

Gwamnatin Najeriya ta soke shirinta na gina katafaren dandalin shirya fina-finai a jihar Kano sakamakon adawar da jama'a suka nuna.


Mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar wakilai, Kawu Sumaila, ya ce shugaban ya saurari koken jama'a musamman malaman addini da suka nuna adawa da lamarin.

Ya kuma nemi masu sana'ar fim da su fahimci halin da gwamnati ta tsinci kanta a ciki.

Batun gina dandalin, wanda aka tsara yi a kauyen Kofa, ya fuskanci suka daga sassa da dama na jihar, inda malamai suka rinka sukar shirin a masallatan Juma'a.

Kazalika kafafen yada labarai sun cika da muhawara kan lamarin, wanda aka shirya zai lashe makudan kudade.

Shi dai Kawu Sumaila ya ce tun asali dama ba Shugaba Buhari ne ya bayar da umarnin gina dandalin ba ko kuma ya ce a sanya sunansa.

Dan majalisar tarayya ne da ke wakiltar yankin ya nemi a yi, ita kuma hukumar shirya fina-finai ta yi yunkurin aiwatarwa saboda yana cikin kasafin kudi na bana.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia