Biyu Daga Cikin Wadanda Za A Nada Jakadu Sun Kasa Yin Taken Nigeria

Yan Majalisu

Biyu Daga Cikin Wadanda Za A Nada Jakadu Sun Kasa Yin Taken Nijeriya


A yayin da ake tantace wadanda za a baiwa mukanin jakadu a majalisar dattijai a jiya Talata, biyu daga cikin wadanda za a baiwa mukaman sun gagara yin taken Nijeriya, wato 'National Anthem'.

A lokacin da shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisa, Sanata Monsurat Sunmonu, ta bukaci daya daga cikin wadanda za a baiwa mukamin wadda ta fito daga yankin Anambra, wato Vivian Nwunaku Okeke da ta yi taken Nijeriya, sai ta kwafsa inda aka samu gyara a ciki.

Haka shi ma daya daga cikin su wanda ya fito daga jihar Neja, mai suna Ibrahim Isa shi ma ya gagara furta taken yadda ya kamata.

Daya daga cikin membobin kwamitin, Sanata James Manager ne ya yi musu gyara.

Har zuwa yanzu dai ana kan tantance mutane 47 da shugaba Buhari ya aiko domin ba su mikamin jakadun.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia