Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Buhari Bai Sanda Batun Gina Dandalin Film Village Ba


Sanata Abdulmimini Jibril

Buhari Bai Sanda Batun Gina Dandalin Film Village Ba


Majalisar wakilan Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari bai sanya gina katafaren dandalin fim a Kano cikin kasafin kudin shekarar 2016 ba, tana mai cewa wani dan majalisa ne ya cusa shirin cikin kasafin kudin.

A karshen makon jiya ne dai mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin majalisar wakilai, Kawu Sumaila, ya ce gwamnatin tarayya ta soke shirin gina dandalin bayan sukar da ta sha daga wajen wasu Malaman addinin Musulinci na jihar wadanda suka ce yin hakan zai gurbata tarbiyyar jama'a.

Batun dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kan dacewa ko rashin dacewar gina dandalin.

Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya shaida wa BBC cewa tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Abdulmumini Jibrin ne ya cusa aikin gina dandalin a cikin kasafin kudi ba tare da sani ko izinin bangaren shugaban kasa ba.

Amma bamu samu jin ta bakin Abdulmumini Jibrin ba domin jin gaskiya ko akasin ikirarin da mai magana da yawun majalisar ya yi ba.

Rikici ya barke a majalisar ta wakilai bayan cire Abdulmumini Jibrin daga shugabancin kwamitin kasafin kudin.

Dan majalisar ya yi zargin cewa an sauke shi ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar da za ta bayar da rigar-kariya ga shugabannin majalisar wakilan da ta dattawa.

Mista Jibrin ya kara da cewa "Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu 40bn a cikin 100bn da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta Najeriya.

Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga mumakin shugaban kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia