Buhari : Tattalin Arzikin Nigeria Zai Ci Gaba Da Tabarbarewa

Buhari : Tattalin Arzikin Nigeria Zai Ci Gaba Da Tabarbarewa


Gwamnatin Najeriya ta ce akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma baya a karon farko cikin sama da shekaru 20.

Ministan tsare-tsaren tattalin arzikin kasar Mr. Udoma Udo Udoma shi ne ya bayyana haka a wata hira da BBC a karshen taron Majalisar koli ta tattalin arzikin kasar da aka gudanar ranar Alhamis.

A makon nan ne Asusun Bayar da lamuni na duniya ya rage hasashen ci-gaba tattalin arzikin kasar na wannan shekara daga kashi 2.3 zuwa kashi 1.8.

Hakan ya faru ne saboda raguwar kudaden shigar da ake samu daga sayar da danyen mai da raguwar wutar lantarki da kuma rashin saka jari.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia