Buhari Ya Sake Bada Umarnin A Tuhumi Wasu Manyan Hafsoshin Soji

buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umarni a binciki wasu manyan tsofaffin jami'an rundunar sojin kasar saboda zargin su da sace kudin sayen makamai.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin da aka kafa domin bincike kan yadda aka sayi makaman, AVM Jon Ode mai ritaya, ya fitar ta ba da shawarar a binciki manyan tsofaffin jami'an rundunar sojin kasar.

Cikin wadanda za a kara bincika har da tsofaffin shugabannin rundunar sojin kasar Laftanar Janar Azubuike Ihejirika da Laftanar Janar Kenneth Minimah.

Mutanen biyu na cikin mutum 54 da za a yi bincike a kansu saboda zargin sace biliyoyin Naira da aka ware domin sayen makaman yaki da kungiyar Boko Haram.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin ne sakamakon shawarar da kwamitin, wanda ya yi bincike kan yadda aka sayi makamai a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, ya ba shi bayan ya gano "cuwa-cuwar da aka tafka".

A cewar shugaban kwamitin, kudin da aka kashe wajen sayen makamai a lokacin sun kai N185, 843,052,564.30 da $685,349,692.49.

Wasu daga cikin mutanen da ake zarga da hannu a badakalar sayen makaman su ne: Tsohon karamin ministan harkokin waje Dr Nurudeen Mohammed, da tsofaffin sakatarorin ma'aikatar tsaro - Alhaji Bukar Goni Aji, Alhaji Haruna Sanusi da Mr E O Oyemomi.

Kazalika, an bayar da shawarar bincikar Kanar Olu Bamgbose mai ritaya na kamfanin Bamverde Limited; Mr Amity Sade na kamfanin Doiyatec Comms Nigeria Ltd; kamfanin DYI Global Services da Mr. Edward Churchill na kamfanin Westgate Global Trust Ltd.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia