Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Buhari Zai Kaddamar Da Sabuwar Rundunar Yaki Da Barayin Shanu A Jihar Zamfara


Shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa ta daura damarar fatattakar 'yan fashin shanu da suka addabi jama'a.


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai wata ziyara a jihar Zamfara da ke arewa-maso-yammacin kasar.


A lokacin ziyarar, shugaba Buhari zai kaddamar da wata sabuwar rundunar yaki da 'yan fashin shanu da suka addabi yankin inda ya ce gwamnatin sa ta daura damarar fatattakar 'yan fashin shanu da suka addabi jama'a.

Daruruwan mutane ke mutuwa a kowace shekara a jihar sakamakon ayyukkan 'yan fashin masu dauke da muggan makamai a kauyukan jihar.

Wannan dai na zuwa ne 'yan makonni bayan da wani tsohon dan majalisar dattawan kasar daga jihar ya yi kira ga shugaban kasar da ya ayyana dokar-ta-ɓaci a jihar har sai tsaro ya inganta.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia