Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Fati Nijar Ta Zama Gimbiyar Mawakan Borgu
A ranar wannan Juma’ar da ta gabata ne Sarkin Borgu da ke jihar Neja a Najeriya, Barista Mohammad Sani Halliru Kitoro, ya nadawa fitacciyar zabiyar nan, Binta Labaran wadda aka di sani da Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Borgu.

A yayin bikin nadin, Mai Martaba sarkin, ya bayyana cewa tun kafin mahaifinsa, Sanata Halliru Kitoro ya rasu ya yi alkwarin baiwa mawakiyar wannan sarauta, amma cikin ikon Allah sai ba a yi bikin nadin ba har ya rasu. Don haka ne dan nasa ya cika alkawarin da mahaifinsa ya daukarwa mawakiyar.

An yi bikin nadin sarautar a fadar mai martaba sarkin Borgu da ke jahar Nejar Najeriya.

Muna yi wa zabiya Fati Nijar fatan alkhairi. Allah kuma ya kara girma ga makiyar Girma-Girma!


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia