Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Filin Girke Girke Yadda Ake Yin Miyar Wake


Miyar-Wake


Filin Girke Girke Yadda Ake Yin Miyar Wake


Abubuwan da za a bukata

1= Wake
2= Man ja
3= Attarugu
4= Gasasshen kifi (banda)
5= Albasa
6= Gishiri da magi
Hadi

Idan uwargida ta samo wakenta, sai ta jika shi. Bayan haka, sai ta Zauna Ta cire kowar jikin waken Ta Tsaftaceshi .

Sai ta dora ruwa a wuta. Bayan ya tafasa, sai ta zuba waken ya yi ta tafasa, har sai ya nuna ya dahu yayi lukwi.

Sannan sai ta zuba yankakkiyar albasa da jajjagaggen attarugu da manja da kifi banda (wankakke).

Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na tsawon mintuna kadan, sannan sai ki zuba magi da gishiri.

Daganan saiki dan kara jira kadan tadan dada tafasa domin gishiri da maginda kika zuba suma su samu wurin zama a muhallinsu .

Shikenan da zaran kinga alamun miyar ta kammalu saiki sauke abinki .

Ana iya cin wannan miyar ne da tuwon shinkafa. Kuma an fi son dafa wannan girkin da rana ko da yamma.

Lallai idan maigida ya ci wannan abincin sai kunnensa ya motsa. Da fatan za a girka wa maigida wannan miyar domin armashi da kuma dandano mai gamsarwa!

Share this


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By HausaMedia