Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Gwamnatin jihar kano zata gina gidaje 200 domin masu karamin karfi


Gwamnatin Kano Za Ta Gina Gidaje Dubu Biyu Domin Amfanar Masu Karamin Karfi


Gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwar cewa za ta gina rukunin gidaje har guda dubu biyu, wanda farashin sa zai kai naira milyan 2.7 domin amfanar marasa karfi.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kwamred Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da kungiyar 'yan jaridu na shiyyar Arewancin kasar nan.

Kwamred Garba ya kara da cewa an kudiri aniyar gina gidajen ne bayan nazarin da gwamnatin ta yi kan gidajen da gwamnatin jihar wadda ta gabata ta gina sun yi tsada wanda hakan ke nuna cewa ba an gina su ba ne domin masu karamin karfi.

“Gwamnatin da ta gabata ta gina gida makamancin haka amma farashinsa ya yi tsada. Farashin kudin gidajen ya tashi daga naira milyan 5 zuwa milya 10 har zuwa milyan 15. Duk da dai cewa gidajen kayatattu ne amma kudin su ya yi tsada. Amma shi kuma gwamna Ganduja zai gina na daidai marasa karfi saboda shi a koda yaushe bukatun al'ummarsa ne a gabansa", inji kwamishinan.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia