Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Gwamnati Zata Gina Katafaren Dandalin Shirya Fina-finai A Kano


Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta soma gina wani katafaren dandalin shirya fina-finai a jihar Kano da ke arewacin kasar.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakallah, wanda ya shaida wa BBC hakan, ya kara da cewa za a fara ginin ne a karshen watan nan na Yuli, inda za a yi shi mataki-mataki.

A cewarsa, "Katafaren dandalin shi ne zai kasance na farko a Najeriya, kuma na biyu a Afirka. Masu shirya fina-finai daga kowacce kusurwa ta duniya za su iya zuwa Kano domin yin amfani da dandalin."

Afakallah ya kara da cewa za a kashe sama da Naira biliyon uku wajen gina dandalin, yana mai cewa ana sa ran fiye da mutum 10,000 za su samu aiki idan aka kammala aikin.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kanon ya ce wannan mataki zai inganta dangantakar da ke tsakanin masu shirya fina-finai na duniya da takwarorinsu da ke Najeriya.

Fina-finan da ake yi a Najeriya dai na cikin hanyoyin da kasar ke amfani da su domin samun kudin-shiga, kuma ko da a shekarar 2014 sai da aka sanya harkar fina-finan a matsayin daya daga cikin hanyoyin da suka fi samar wa kasar kudin-shiga.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia