Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Hadisai Goma Sha Tara 19 Masu Bushara Da Gidan Aljannah


Hadisai Goma Sha Tara 19 Masu Bushara Da Gidan Aljannah


HADISI NA FARKO

Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa kata faren gida a gidan Aljanna sai Sayidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawai tawa sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa.

HADISI NA BIYU

Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.

HADISI NA UKU

Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai ciyayeshi daga fitinar dujal.

HADISI NA HUDU

Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta ayatal kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba.

HADISI NA BIYAR

Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka da daddare to ka karanta kulya ayyu hal kafirun to bazaka mutu mushriki ba a idan ka mutu a wannan dare.

HADISI NA SHIDA

Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya ce Ash-hadu wahadahu lasharika lahu wa anna muhammadan Abduhu wara suluhu. Allahumma Jaalni minattauwabina wajaalni minal mutadhahhirina.

Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar sa to zaa bude masa kofofin Aljanna guda takwas ya zabi wadda ya ke son shiga.

HADISI NA BAKWAI

Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma Wabihamdika ash-hadu allah Ilaha illallah anta astagfiruka waatubu ilaika.

Zaa rubuta wannan acikin wata takarda bazaa bude ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta.

HADISI NA TAKWAS

Wani sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu Akbar kabira, Walhamdulillahikasira, Wasubhanallahi bukratan waasila, Sai manzon Allah ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan kalma sai ya ce ni ne Ya rasulullah sai manzon Allah ya ce nayi mamakin wadan nan kalma da ka fada, anbude rofofin sama gaba daya saboda wannan kalma da ka fada. Sai Abdullahi Dan Umar ya ce tun daga wannan rana kullum sai na fadi wannan kalma, ban taba tsallake wata rana ko wani lokaci da bana fadar wannan kalma ba.

HADISI NA TARA

Wata rana mun kasance muna Sallah a bayan manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga rukuu sai ya ce Samiallah Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Rabbana Walakal Hamdu, Mandan Kasiran Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutum ya ce Ni ne ya manzon Allah Sai manzon Allah ya ce Naga malaika taladin da yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.

HADISI NA GOMA

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Wanda ya yi sallar nafila rakaa goma sha biyu tsakanin dare da rana Allah zai gina masa gida a cikin gidan Aljanna.

HADISI NA SHADAYA

Wanda ya kiyaye yanayin nafila rakaa hudu kamin sallar azahar da kuma rakaa hudu kamin sallar laasar to Allah zai haramta masa shiga wuta.

HADISI NA SHA BIYU

Manzon Allah Yana cewa Allah ya jikan wanda ya jikan wanda ya yi sallar nafila rakaa hudu kamin laasar.

HADISI NA SHA UKU

Wanda yake karanta ayoyi goma da daddare to bazaa rubuta shi cikin gafalallu ba wanda ya ke karanta ayoyi dari to zaa rubuta shi cikin masu bauta ga Allah, wanda kuma ke karanta ayoyi dubu a cikin dare kullum to zaa rubuta shi daga cikin masu arzikin lahira.

HADISI NA SHA HUDU

Wanda da yi Sallar nafila a cikin duhu inda bawanda zai ganshi to Allah zai linka masa sau ashirin da biyar na sallar da zai yi wani ya ganshi.

HADISI NA SHA BIYAR

Annabin tsira ya ce Wanda yayi sallar walha (Sallar hantsi/Luha) rakaa hudu kuma yayi rakaa hudu kamin sallar laasar, Allah zai gina masa a cikin aljanna.

HADISI NA SHA SHIDA

Hakika malaiku suna yin salati ga wadanda suke cika sahun farko, idan suka ga wata kafa a cikin Sallah suna cikata basa barin ta kuma Allah zai cika darajar sa da kimarsa da martabar sa.

HADISI NA SHA BAKWAI

Babu wani Bawa da zai yi sujada ga Allah face Allah ya rubuta masa lada ya kankare masa zunubi ya kuma daukaka masa daraja don haka mu yawaita sujjada.

HADISI NA SHA TAKWAS

Wanda yayi sallar asuba a cikin jami sannan ya zauna yana ta salati yana ta ambaton Allah bai bari ba harsai da rana ta fito, sannan ya tashi yayi sallar walha rakaa biyu to Manzon Allah ya ce Kamar yayi hajji cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! hajji cikakke! hajji cikakke! hajji cikakke! Haka Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallama ya mai maita.

HADISI NA SHA TARA

Manzon Allah ya ce wanda ya yi Sallah arbain a cikin jami maana kwana takwas jami bai tsere masa ba, sallolin nan biyar a jere duk da shi ake kabarta kabbarar harama, to Allah zai rubuta masa kubuta daga musibu guda biyu na farko Allah zai rubuta masa kubuta daga wuta bazai shiga wuta ba, na biyu kuma Allah


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia