Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Hotuna : Matashin Daya Kirkiri Taractor A Nigeria Terfa Timothy AddingiA Nigeria wani matashi dan jihar Benue ya kirkiro wata karamar motar noma, wato Tarakata ko Tantan wadda dukkan kayan da aka yi amfani da shi wajen kera ta a Najeriya aka yi shi.


Shi dai matashin, mai suna Terfa Addingi ya ce, ya kirkiri Taraktar ne domin saukaka wa kananan manoma hidimar gona.

Tuni da aka jarraba motar domin tabbatar da ingancinta.


Terfa Addingi, ya ce, yana fatan samun tallafi domin fadada kamfanin da zai rika kera Taraktar, wanda ta hakan yake fatan samar da aikin yi ga wasu matasan.

Motar da matashin ya kirkira ta Tarakata dai mai saukin sarrafawa ce wadda mata ma za su iya tuka ta, kuma ya dauki tsawon watan biyu ne kawai yana hada motar.

KALLA CIKIN HOTUNA...


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia