Hukumar EFCC Ta Cika Hannu Da Tsohuwar Shugaban Sashin Hausa Na BBC

Jamila Tangaza

Hukumar EFCC Ta Cika Hannu Da Tsohuwar Shugaban Sashin Hausa Na BBC

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya-EFCC ta kama shugabar sashin kula da mallakar filaye a hukumar mulki ta babban birnin Najeriya, Abuja, Hajiya Jamilah Tangaza bisa zargin karkatar da wasu kudade na gwamnati.

Wata majiya daga EFCC ta shaida wa BBC cewa ana zargin Jamilah Tangaza ne wadda ta shiga hannun hukumar tun ranar Laraba, da karkatar da kudaden da suka kai Naira miliyan 150.

Majiyar ta ce an yi amfani da kudaden ne wajen sayen wani gida a gundumar Asokoro a Abuja, inda aka yi amfani da wasu kamfanoni da ke da alaka da ita.

Yunkurin BBC na jin ta bakin Jamilah Tangazar bai yi nasara ba, saboda wayar salularta ba ta tafiya, kuma babu amsar sakon "text" da aka aika mata.

Majiyar EFCC ta ce hukumar na bincikar Hajiya Jamilah ne, bayan ta samu bayanai kan bacewar kudaden, kuma ba ta gamsu da bayanan da Jamilah Tangazar ta yi mata ba kan tuhumar.

A cewar majiyar, duk da rashin gamsuwa da bayananta, hukumar EFCC ta bayar da belinta.

Sai dai hukumar ta EFCC tana ci gaba da tsare ta saboda ba ta cika sharuddan belin na ta ba.

Jamilah Tangaza dai tsohuwar shugabar sashin Hausa na BBC ce, ta kuma kasance mataimakiya ta musamman ga tsohon ministan babban binin Nigeria Abuja, kafin daga baya ta zama shugabar sashin kula da mallakar filaye ta babban birnin tarayyar.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia