Jakadan Amurka Yayi Biris Da Gayyatar Majalisa Domin Bada Shaida-Nigeria


Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ne ya bayar da umarnin yin binciken

Majalisar dokokin Najeriya ta kasa gudanar da sauraron bahasi kan zargin neman karuwai da ake yi wasu 'ya'yanta sa'adda suke je wata ziyara a kasar Amurka, bayan da jakadan Amurka a kasar ya ki bayyana a gabanta.

A ranar Alhamis ne dai majalisar ta shirya karbar hujojin da Ambasada James Entwistle ya ce yana da su, wadanda ke nuna cewa 'yan majalisar sun nemi karuwai a kasarsa a watan Mayu.

Amma jakadan ya ki bayyana a gaban majalisar bisa hujjar cewa yana da rigar kariya, sai dai idan shi ya so yin hakan bisa radin kansa.

Shi ma dai ministan harkokin wajen Najeriyar da aka tsara zai bayyana tare da Mista Entwistle bai samu bayyana ba saboda yana kan wata ziyara a birnin Kigali na kasar Rwanda.

Mai magana da yawun majalisar Abdurrazak Namdaz, ya shaida wa BBC cewa majalisar ta dage zaman har zuwa ranar 20 ga wannan watan bayan ministan harkokin wajen ya dawo daga tafiyar da ya yi.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia