Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Jakadan Amurka Zai Bayyana Hujjoji Gaban Majalisa Bisa Zargin Neman Karuwai


Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci jakadan Amurka a kasar James Entwistle, ya bayyana a gabanta domin yin karin bayani kan zargin da ya yi wa wasu 'yan majalisar wakilan da bigewa da neman karuwai a lokacin da suka kai wata ziyarar aiki kasar.

Wata wasika da Mista Entwistle ya aike wa shugaban majalisar wakilan, Yakubu Dogara, ya zargi 'yan majalisa uku daga cikin goma da suka kai ziyara kasar da nuna rashin kamala da yunkurin yin fyade da neman karuwai.

A cewar Mista Entwistle 'yan majalisar su ne: Mohammed Garba Gololo (APC, Bauchi), Samuel Ikon (PDP, Akwa Ibom) da kuma Mark Gbillah (APC, Benue).

Ya kara da cewa Mohammed Garba Gololo ya yi yunkurin rungumar wata ma'aikaciya da ta je gyara masa dakinsa da zummar yin lalata da ita.

Mista Entwistle ya kara da cewa, "Mark Terseer Gbillah da Samuel Ikon sun bukaci ma'aikatan wurin ajiye motoci na otal din da su nemo musu karuwai."

Tun a wancan lokacin ne dai 'yan majalisar suka musanta zargin, inda suka ce a shirye suke su koma Amurka domin kare kansu.

Kazalika, 'yan majalisar sun bukaci jakadan Amurka ya janye zargin ko kuma su shigar da kararsa a kotu.

Lamarin dai ya sa majalisar ta kafa kwamitin bincike, wanda ya nemi Mista Entwistle ya bayyana a gabanta ranar Laraba da Alhamis, domin gabatar da hujjojinsa kan zarge-zargen da ya yi wa 'yan majalisar.

Shugaban kwamitin da'a na majalisar Nicholas Ossai, ya ce ba su gayyaci jami'an otal din da aka yi zargin 'yan majalisar sun nemi karuwan a cikinsa ba, yana mai cewa gayyatar da suka yi wa Mista Entwistle ta wadatar.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia