Kama Na Hannun Damar Buhari Ya Harzuka Lauyoyi Kan EFCC

Umar Muhammed

Tsare Na Hannun Damar Buhari Ya Harzuka Lauyoyi Kan EFCC


Daga Ahmed Abdullahi

Wasu lauyoyi a karkashin kungiyar lauyoyi masu kare tsarin dimokradiyya sun kaddamar da kamfen ganin hukumar EFCC ta sako daya daga cikin 'ya'yan kwamitin Shugaban kasa wanda ya binciki badakalar makamai, Umar Mohammed.

Wakilinmu ya ruwaito cewa kungiyar lauyoyin sun bi lunguna da sako- sako na babban birnin tarayya inda suka lika fastoci da ke dauke da hoton Umar Mohammed da kuma sakon cewa EFCC
ta sako shi kasancewa kotu ta bukaci hakan.

Idan ba a manta ba, kwanaki ne Shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya( DSS) ya kai karar Umar Mohammed wanda tsohon sojan sama ne kan cewa yana amfani da sunan Shugaban kasa kasancewarsa daya daga cikin 'yan kwamitin binciken badakalar makamai inda yake karbar kudi daga wadanda ake zargi.

A wancan lokacin sauran 'yan kwamitin sun koka bayan da Shugaban kasa ya bayar da umarnin a tsare shi inda suka nuna cewa an gabatar da zargin don a muzanta sakamakon binciken kwamitin wanda ya gano yadda aka sace bilyoyin Naira da sunan sayo makamai tun daga zamanin Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa 'Yar adua.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia