Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Shin Ko Kasan Cewa Bacci Babbar Ni'ima Ce Ga Rayuwar Dan AdamMe kuka sani dangane da irin halin da jikin mutun yake a dai-dai lokacin da mutun yake bacci? Dr. Michael Breus, likitan kwakwalwar dan’adam ne a wani asibiti mai zaman kanshi a kasar Amurka. Ya bayyanar da sakamakon wani bincike da suka gudanar dake bayyanar da wadansu abubuwa da jikin mutun kanyi a dai-dai lokacin da mutun yake bacci.

A lokacin da mutun yake bacci, dimin yanayin jikin shi kan sauka, inda yakeyin sanyi. Hakama duk acikin bacci mutun na rage nauyi, domin kuwa ruwan dake jikin mutun yariga ya fita don zama fitsari, haka nunfashin da mutun kanyi yana kara rage kitsen dake jikin mutun. Da yawa musamman ga yara a dai-dai lokacin da suke bacci kasusuwan jikin su suke kara mikewa don kara tsawo da karfi.

Wannan lokacin zuciya nasamun hutu yadda ya kamata da har jinin mutun kan sauka, hakama duk gabobin jiki suna mutuwa a wannan lokacin. Idan har mutun yana bacci kwayar idon shi takanyi yawo fiye da idan baya bacci, wanda hakan kansa mutun indan ya tashi daga bacci sai yaga kwantsa a idon shi, bacci yana taimakawa wajen wanke duk wasu kananan cuttutuka da hakukuwa da suka shiga cikin ido da rana.

Hakama a lokacin da mutun yake bacci duk wasu jijiyoyin jikin shi kan mike wajen gudanar jinni a ko ina, hakan na taimakawa matuka wajen fitar wasu cuttuka daga jikin mutun, kana fatar jikin mutun na samun karuwar lafiya saboda gudanar jinni da kuma iska mai inganci dake shiga ta kafofin jiki.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia