Sojoji Sun Bace Bayan Yan Boko Haram Sunyi Musu Kwanton Bauna

Sojoji Sun Bace Bayan Yan Boko Haram Sunyi Musu Kwanton Bauna


Rundunar sojan Nigeria ta ce wasu dakarunta sun ɓace a jihar Borno, bayan da 'yan Boko Haram suka yi musu kwanton-ɓauna a ƙauyen Guro Gongon.

Kakakin rundunar sojan Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya shaida wa BBC cewa dakarun na su suna kan hanyar komawa sansanin su ne, bayan sun je farautar 'yan Boko Haram, inda suka kuma samu gagarumar nasara.

Kuka-Sheka ya ce sojojin sun kashe 'yan Boko Haram da dama, sun kuma kwato manyan makamai da kanana da kayan abinci, sannan kuma suka lalata maɓoyar 'yan Boko Haram din.

Jami'in ya ce a kan hanyar dakarun na su ne ta komawa sansaninsu, wasu 'yan Boko Haram suka yi wa sojojin kwanton-ɓauna, inda aka yi mummunar musayar wuta, aka kashe 'yan Boko Haram da dama, yayin da a ɓangaren sojoji kuma aka ji wa 19 rauni, sannan aka kuma ji wa wasu civilin JTF su uku da ke yi wa sojoji rakiya rauni.

Kanal Kuka-Sheka yace a nan ne kuma da dama daga dakarun na su suka ɓace, to sai dai yace daga baya wasu sun fara komawa sansanin na su.

Kakakin ya ce an tura wasu sojojin ƙundumbala domin nemo sojojin da suka ɓace.

Sai dai bai bayyana cewa ko 'yan Boko Haram ne suka kama sojojin ba, kuma bai bayyana adadin sojojin da suka ɓace ba, sannan bai bayyana cewa ko an kashe wasu daga cikin su ba.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia