Sojoji Sun Fara Luguden Wuta Akan Tsagerun Niger Delta - Nigeria


Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewa dakarunta sun kai hari ta sama kan tsagerun yankin Naija Delta a yankin Arepo na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar.


Sai dai kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Rabe Abubakar, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, bai yi karin bayani kan yawan tsagerun da aka kashe ba.

Ya kara da cewa rundunar sojin kasar ba za ta ci gaba da barin mayakan suna cin karensu babu babbaka ba.

Mazauna yankin na Alepo da ma na wasu yankunan jihar Lagos da ke makwabtaka, suna cikin farbaga kan hare-haren da 'yan yankin Naija Deltan ke kai musu a baya bayan nan.

Rahotanni sun ce mayakan sun kashe mutane da dama a hare-haren da suka matsa kaiwa a yankin.

Tsagerun yankin na Naija Delta dai sun matsa wajen fasa bututan man fetur a baya bayan nan, lamarin da ya sa man da kasar ke fitarwa ya ragu matuka, ya kuma jefa Najeriya cikin duhu sakamakon rashin hasken wutar lantarki saboda rashin samun iskar gas din da na'urorin samar da lantarkin ke amfani da ita.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia