Yadda 'Yan Social Media Sukayi Tasiri Wurin Soke Batun Gina Film Village A Kano

film village

Yadda 'Yan Social Media Sukayi Tasiri Wurin Soke Batun Gina Film Village A Kano


Muhawarar da aka rika tafkawa a shafukan sada zumunta na zamani kan dacewa ko rashin dacewar gina katafaren dandalin yin fim a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen soke shirin.

Tun bayan da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Isma'ila Na'abba Afakallah ya bayyana shirin gina dandalin ne mutane suka fara bayyana ra'ayoyin da suka sha bamban da juna game da dandalin.

Sai dai kuma batun ya kara daukar hankalin mutane ne bayan gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da gina dandalin a makon jiya.

Tun daga ranar ne shafukan sada zumunta suka cika makil da ra'ayoyi daban-daban kan batun.

Wasu dai sun goyi bayan wannan mataki, inda suka bayyana shi da cewa wata hanya ce da za ta bunkasa harkar fina-finai a Najeriya da samar wa dubban mutane ayyukan yi.

Hasalima, a cewarsu, wannan ne karo na farko da za a samu ayyukan yi masu yawan da ba a taba samu ba a lokaci guda ta hanyar irin wannan harka.

Muhammadu

Gwanati ta bukaci 'yan fim su fahimci halin da take ciki

Masu irin wannan ra'ayi sun kirkiro wani maudu'i da a turance ake kira #IStandWithFilmVillage, wato Ina Goyon Bayan Gina katafaren dandalin fim, domin aikewa da sakonninsu.

Sai dai masu adawa da wannan mataki sun yi kaimi wajen bayyana abin da suke gani illa ce game da gina katafaren dandalin fim din.

Yawancin masu irin wannan ra'ayi suna nuna cewa hakan zai kara ruguza tarbiyyar Kanawa, wadanda dama wasun su ba sa ga-maciji da masu harkar fina-finai.

Su ma sun kirkiri na su maudu'in mai taken #WeSayNoToFilmVillage, wato muna adawa da gina dandalin fim a jihar Kano.

Sai dai da alama babban abin da ya taka wa gwamnatin kasar birki dangane da gina wannan dandali shi ne sukar da Malamai suka rika yi wa shirin.

Fitattun Malaman jihar, irin su Muhammad Bin Uthman na masallacin Sahaba da Dr Abdullahi Usman na masallacin Gadon Kaya sun yi huduba a ranar Juma'a, suna masu sukar shirin.

Mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar wakilai, Kawu Sumaila, ya ce shugaban ya saurari koken jama'a musamman malaman addini da suka nuna adawa da lamarin.

Ya kuma nemi masu sana'ar fim da su fahimci halin da gwamnati ta tsinci kanta a ciki.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia