Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Yan Kannywood Sun Koka Kan Batun Sauke Ginin Film Village A Kano

film village

Yan Kannywood Sun Koka Kan Batun Sauke Ginin Film Village A Kano


Malamai sun ce gina dandalin zai gurbata tarbiyya

Fitattun jaruman fina-finan Kannywood da masu ruwa da tsaki a harkar fim sun ce malamai sun yi wa shirin gwamnatin tarayya na gina katafaren dandalin fim a jihar Kano gurguwar fahimta.

A ranar Lahadi ne dai mai bai wa shugaban kasar Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar wakilai, Kawu Sumaila, ya ce an soke shirin ne bayan shugaban ya saurari koken jama'a musamman malaman addini da suka nuna adawa da lamarin.

Malaman dai sun ce gina dandalin zai gurbata tarbiyyar jama'a.

Fitattun Malaman jihar, irin su Muhammad Bin Uthman na Masallacin Sahaba da Dr Abdullahi Usman na Masallacin Gadon Kaya sun yi huduba a ranar Juma'a, suna masu sukar shirin.

Sai dai fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu, ya shaida wa BBC cewa soke dandalin ya daure masa kai.

A cewarsa, "Ban ga yadda gina dandalin fim zai bata tarbiyya ba. Ta yaya malamai za su ce haka bayan yawancin fina-finan da muke yi sai mun nemi shawararsu sannan mu yi.

Su sun sani cewa muna aiki da duk gyaran da suka yi mana a harkar fim, kuma idan ka duba za ka ga an samu sauyi kan yadda ake yin fina-finai yanzu".

Shi ma fitaccen jarumi kuma darakta, Falalu Dorayi, ya shaida wa BBC cewa ba su ji dadin soke gina dandalin fim din ba, yana mai cewa mutane sun yi wa shirin gurguwar fahimta.

Ya ce, "Ya kamata mutane su sani cewa dandalin ba wurin holewa ba ne; wuri ne da za a dauko kwararren mutum a ba shi shugabancinsa, kamar yadda aka yi a hukumar tace fina-finai.

Za a bar 'yan fim su gina garuruwa ta yadda duk rawar da za a taka a kowanne fim ba sai an je wani wurin ba za a yi a can. Mutane ba su tambayi yadda za a gudanar da wurin ba, amma suke ta sukar shirin."

Ya kara da cewa da an gina dandalin da dubban mutane sun samu ayyukan yi.


0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia