Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Abubakar Shekau Yace Al-Barnawi Kasur Gumin Mushiriki Ne

Abubakar Shekau

Abubakar Shekau Yace Al-Barnawi Kasur Gumin Mushiriki NE.

Tsohon Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya yi watsi da matakin maye gurbin sa da kungiyar masu fafutukar kafa daular Musulunci a Iraqi da Syria wato IS ta yi da wanin sa.

A jiya laraba ne aka nada Abu Mus'ab al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar IS reshen yammacin Afurka.

Amma Abubakar Shekau wanda aka shafe shekara guda ba ji duriyar sa ba, da sauran magoya bayan sa, sun kira sabon shugaban da mushuriki ne da ya kaucewa tafarkin da kungiyar Boko Haram ke kai.

Ya kuma jaddada ce wa shi da magoya bayan sa su na nan kan akidar su.0 comments:

Post a Comment

HausaMedia.Com |™ Hausa News And Entertainment Blog | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Modify By HausaMedia